IQNA

An Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Iran

23:59 - April 19, 2018
Lambar Labari: 3482587
Bangaren gasar kur’ani, A yau Alhamis ne ake bude taron babbar gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta duniya a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an bude babban taron gasar kur’anin ne tare da halartar manyan jami’an gwamnatin Iran da kuma manyan baki daga kasashen duniya, haka nan gasar dai ana gudanar da ita ne sau daya a kowace shekara, kuma wannan shi ne karo na talatin da biya da ake gudanar da gasar a kasar Iran.

Babban kwamitin shirya gasar ya sanar da cewa, za a gudanar da gasar kamar yadda aka gudanar da ita a shekarar da ta gabata inda aka kasa gasar zuwa bangaren maza da mata sai bangaren masu nakasa da makafi, wadanda suka fito daga kasashen duniya daban-daban da suka hada da na musulmi da ma wadanda ba na musulmi ba.

Bayanin ya kara da cewa adadin dukkanin wadanda za su halrci a gasar a dukkanin bangarorinta za su kai mutane dari uku da saba’in, da suka hada da na ciki da wajen kasar.

Tsawon mako guda ne za a skwashe ana gudanar da gasar, kuma daga karshe za a fitar da matsayi na daya da na biyu da na uku daga kowane rukuni, kuma za a bayar da kyautuka na bai daya ga dukkanin mahalarta gasar, da kuma kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a dukkanin bangarorin gasar.

Bisa ga al’ada dai bayan kammala gasar baki da suka zo daga kasashen duniya sukan gana da jagoran juyin juya halin musulunci na kasar Iran, daga nan kuma za su ziyarci wasu muhimman wurare na addini da na tarihi, kafin su koma kasashensu.

3707118

An Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Iran

An Bude Gasar Kur’ani Ta Duniya A Kasar Iran

 

captcha